A kalla mutane 12 ne aka bayar da rahoton sun mutu a wani sabon harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a kauyen Garubula da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Wani mazaunin garin na Garubula da ke yankin Biu a jihar ta Borno mai suna Usman Bunu ya ce, maharan sun halaka sarkin garin, wani dogari da kuma wasu mutane 11. Ya ce, mayakan sun shiga garin ne da tsakar daren ranar Laraba, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi tare da gargadin mazauna garin da su fice.
Wani jami'in tsaro wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an gargazaya da sarkin garin zuwa asibiti da ke kusa kafin daga bisani ya ce ga garinku.
Sai dai jami'an tsaro sun bayyana cewa, babu wanda aka kama ya zuwa yanzu dangane da wannan hari, yayin da mayakan suka arce zuwa wani daji dake kusa da kauyen. (Ibrahim)