Ministan harkokin wajen kasar Tunisiya Mongi Hamdi ya sanar a ranar Labara cewa, akwai yiyuwar rufe kan iyakokin kasar Tunisiya da kasar Libya idan har rikici ya cigaba da tsananta a kasar Libya. Kuma ya zama dole daga wajen ministocin harkokin wajen kasashen dake makwabtaka da kasar Libya su cimma wata mafitar hadin gwiwa domin magance tabarbarewar matsalar tsaro a cikin wannan kasar, in ji Hamdi a yayin da yake hira tare da manema labarai a ma'aikatarsa.
A cewar shugaban diplomasiyyar Tunisiya, karamin ofishin jakadancin Tunisiya dake Tripoli zai rufe kofa idan rikicin Libya ya cigaba da tsananta.
Amma wata cibiyar jakadancin daga bangaren hanyar Ras Jedir dake kudu maso gabashin Tunisiya za ta taimaka wajen wucewar 'yan kasar Tunisiya dake fitowa daga yankunan kasar Libya, in ji mista Hamdi.
Da yake tabo batun yawan 'yan Libya dake kwarara zuwa Tunisiya domin tsirar da rayukansu daga yake-yaken da kasarsu take fuskanata, ministan Tunisiya yayi kashedin cewa, rashin kudi da ja da bayan tattalin arzikin Tunisiya ba za su taimaka ba wajen karbar wadannan 'yan gudun hijiran Libya. (Maman Ada)