Gwamnatin Afrika ta Kudu ta kawar da duk wani matakin tura sojoji a kasar Lesotho, dake fama da tashe-tashen hankali dake da nasaba da rikicin siyasa. Ministar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu, madam Maite Nkoana-Mashabane, ta bayyana cewa, duk wani matakin tura sojoji a Lesotho, makwabciyar kasa abu ne da ba ya bisa hanya, duk da cewa, an jibge jami'an tsaro a sassan kasar, da ma kuma kewayen Maseru, babban birnin kasar.
Ba mu da wata yarda kan tura sojoji, amma kuma, muna daga cikin kasashen da suka dauki niyyar tura sojoji a Afrika bisa sa kai, in ji madam Maite Nkoana-Mashabane, ministar harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu. (Maman Ada)