in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar sojin ruwan Sin ta isa gabar ruwan Namibia
2014-06-12 15:07:23 cri

Tawagar sojojin ruwan kasar Sin mai ba da kariya ga jiragen ruwa, ta isa tashar jiragen ruwa ta "Walvis Bay" dake kasar Namibia, a ziyarar sada zumunci da ta kai wannan yanki na kudu maso yammacin nahiyar Afirka.

Cikin jawabinsa na maraba ga tawagar, jakadan kasar Sin a kasar ta Namibia Xin Shunkang, ya ce, wannan ne karon farko da irin wannan tawaga ta isa Namibia, tun bayan da kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar diflomasiyya a tsakanin su shekaru 24 da suka gabata. Don haka a cewar sa, hakan zai karfafa fahimtar juna, da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Shi ma a nasa jawabin, babban hafsan jiragen ruwan kasar ta Namibia Admiral Nghipandwa, cewa ya yi, wannan zayara za ta daukaka matsayin dangantakar dake tsakanin rundunonin ruwan kasashen biyu.

Namibia ce dai kasa ta 7 da wannan tawaga ke ziyarta, cikin kasashen Afirka 8 da ta tsara kewayawa, bayan ta kammala aikinta a gabar "Gulf Aden" da yankunan tekun Somaliya. Wannan tawaga dai ta yiwa jiragen ruwa sama da 5,500 rakiya, a hanyoyin teku masu hadari kwarai tun daga watan Nuwambar bara, ya zuwa watan Afirilun da ya shude. Ana kuma sanya ran isar ta gabar ruwan Afirka ta Kudu a gobe Juma'a, wurin da zai zamo na cikon 8 a ziyarar ta wannan karo. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China