in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta shirya hallaka jirgin ruwa dauke da muggan kwayoyi
2014-08-29 10:27:22 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Keyatta ya ce, zai jagoranci jami'an tsaro domin a nutsar da wani jirgin ruwan wanda aka kama a watan da ya wuce, dauke da muggan kwayoyi na hodar iblis, wacce darajarta ta kai kwatankwacin dalar Amurka miliyan 11.37.

Shugaban kasar ta Kenya ya kara da cewar, gwamnatinsa za ta hallaka jirgin da ya dauko muggan kwayoyin, ba tare da yin wani la'akari da ko wane ne ya mallaki jirgin ba, domin hakan ya zamanto darasi ga mutanen da suka dukufa wajen bata rayuwar yaran kasar.

A watan Yuli ne 'yan sandan kasa da kasa da hukumomin Amurka suka kwarmatawa jami'an tsaron kasar Kenya cewar, jirgin na kan hanyarsa zuwa Kenya, wannan ya sa jami'an tsaron Kenya suka bi jirgin suka kamo shi, sannan suka kai shi tashar jirgin ruwa ta Mombasa inda ya tsaya a karkashin kulawar jami'an tsaro. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China