in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta sha alwashin cin galaba kan tsattsauran ra'ayi domin samun daidaito
2014-07-17 10:03:39 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a ranar Laraban nan 16 ga wata ya ce, gwamnatinsa za ta yi aiki kafada da kafada da sauran abokan kasashe domin yakar tsattsauran ra'ayi da sauran miyagun halayya dake barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al'umma.

Shugaba Kenyatta ya ce, gwamnatin ba za ta kyale miyagun mutane da suke ta kai hare-hare da gurneti da bama-bamai a cikin kasar su boye karkashin 'yancin yin ibada, da kundin tsarin mulkin kasar ya amince da shi ba, suna karya doka.

Ya ce, a shirye gwamnati take kuma ta yi azamar hada hannu da abokan kasashe domin samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a cikin al'umman kasar Kenya.

A lokacin da yake kaddamar da gudunmuwar abincin bude baki ga marasa galihu a fadin kasar da jakadun wadansu kasashe musulmai suka bayar cike da babbar motan kaya, shugaba Kenyatta ya mika godiyarsa bisa ga wannan karamci, ya ce, cikakken 'yancin da dokar kasar ta bayar ya kamata kowa ya more shi yadda ya kamata.

Shugaban na Kenya ya tabbatar wa wadanda suka ba da gudunmuwar wadannan kayan abinci cewar, sakonsu zai isa ga wadanda aka yi wa tanadi a garuruwan da suka hada da Lamu, Mandera, Wajir da Moyale. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China