in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin marasa aikin yi a Kenya ya kai kashi 12.7 cikin 100
2014-07-21 09:57:08 cri

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Kenya, ya bayyana shirin gwamnatin kasar na bullo da wani tsari da zai nazarci matsalar rashin aikin yi da kasar ke fuskanta.

Sakataren tsare-tsare na majalisar zastarwar kasar Anne Waiguru wanda ya bayyana hakan ga taron dandalin matasa na shiyya da aka shirya a Nairobi, babban birnin kasar ta Kenya ya ce, manufar tsarin ita ce samar da guraben aikin yi ga matasan kasar Kenya, da zarar ya samu amincewar majalisar dokokin kasar.

Kamar yadda tsarin ya tanada, daga yanzu sai an nazarci dukkan harkokin zuba jari da ayyukan da za a gudanar a kasar don ganin irin guraben ayyukan da za su samar a kasar kafin a aiwatar da su.

Waiguru ya ce, galibin masu fama da rashin aikin yi matasa ne dake tsakanin shekaru 18-35 wadanda suka kasance sama da kashi 30 cikin 100 na al'ummar Kenya.

Dandalin na tsawon kwanaki biyar, zai hallara shugabannin matasa da masu tsara manufofi inda ake sa ran za su yi nazarin kan matsalar rashin aikin yi da matasan ke fuskanta a shiyyar, tare da kuma bullo matakan magance wannan matsala. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China