Wani dandali na tsakanin 'yan Afrika ta Tsakiya CAR zai gudana a birnin Brazzavile daga ranakun 21 zuwa 23 ga watan Juli bisa kokarin da ake na kawo karshin jin karar makamai da kuma bude hanyar sasantawar siyasa a kasar Afrika ta Tsakiya, in ji sakatare janar na gamayyar kungiyar tattalin arzikin tsakiyar Afrika (CEEAC), Ahmad Allam-Mi, a ranar Litinin a birnin Libreville.
Shiga tsakanin kasa da kasa, a cikin kokarinta, za ta taimakawa 'yan Afrika ta Tsakiya a karon farko wajen cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta da duk wasu tashe-tashen hankali a birnin Brazzaville, da daidaita batun mulkin wuci gadi cikin hadin gwiwa, sannan a karo na biyu, za a cigaba a birnin Bangui da tattaunawar siyasa, ta yadda za'a cimma wata yarjejeniyar karshe ta siyasa domin kawo karshen rikci a kasar, in ji mista Allam-Mi. (Maman Ada)