A ranar Litinin din 28 ga wata, kungiyar 'yan kwadago na kasar Afrika ta Kudu ta amince da tayin da aka mata na karin albashi, abin da zai kawo karshen yajin aiki na sama da makonni uku da ake yi a bangaren karafa da injiniya.
Tayin dai babbar ma'aikatar a wannan bangaren SEIFA ta yi wa kungiyar ta NUMSA, kuma ya kunshi yarjejeniya ta albashin shekaru uku wanda zai karu da kashi 8 zuwa 10 a cikin 100 a shekarar farko. Kashi 7.5 zuwa kashi 10 a shekara ta biyu, sannan kashi 7 zuwa 10 a cikin 100 a shekara ta uku, in ji kakakin kungiyar Marius Croucamp.
Kungiyar ta NUMSA wadda ke jagoranrta yajin aikin ta tabbatar da karban wannan tayin. Kamar yadda wata majiya ta kusa da ita ta yi bayani, dukkan bangarorin sun amince da sashi na 37 na ka'idojin aikin karafa da injiniya, kuma za su ci gaba da kasancewa, tare da fatan duk bangarorin dake karkashinsu sun aiwatar da hakan.
Sashi na 37 dai ya kare hakkin ma'aikata na shiga duk wani nau'in daidaitawa a ma'aikatun, muddin aka rigaya aka cimma matsaya a kan abin da ya jibanci karin albashi da yanayin aikin kasa baki daya. (Fatimah)