in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da bullar Ebola a DRC, in ji WHO
2014-08-28 09:54:28 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, rahotanni daga ma'aikatar lafiyar jamhuriya dimokaradiyyar Congo DRC sun tabbatar da bullar cutar nan mai saurin kisa ta Ebola a wani sashi na kasar.

WHO ta ce, an samu bullar wannan cuta ne a lardin Equateur dake arewacin kasar. Inda wata mata mai juna biyu a kauyen Ikanamongo ta fara nuna alamun kamuwa da ita, bayan da ta sarrafa wani naman daji da mijinta ya kamo, ta kuma rasu a ranar 11 ga watan nan bayan ta sha fama da wani zazzabi mai tsanani.

Kaza lika an samu mutane 24 da suka ziyarci asibiti da irin wannan nauyi na zazzabi tsakanin ranekun 28 ga watan Yuli da 18 ga watan Agustan nan, kuma tuni 13 daga cikin su suka rasu.

Hukumomin lafiyar kasar dai sun tabbatar da yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum, lamarin da ya yi sanadiyar harbuwar wasu daga ma'aikatan kula da lafiya 3, da suka lura da matar mai juna biyu da Ebolar ta hallaka, baya ga wasu karin ma'aikatan asibiti su 2, wadanda su ma daga baya suka rasa rayukan su bayan sun nuna alamun kamuwa da cutar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China