Tawagar MDD da ke gudanar da ayyukanta a Libya za ta rage yawan ma'aikatanta na dan wani lokaci sakamakon matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar.
Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai, ya ce, an yanke wannan shawara ce da nufin kare lafiyar ma'aikatan, kuma da zarar al'amura sun inganta, za a sake duba lamarin.
Kasar ta Libya da ke kokarin shirin koma wa ga tsarin demokiradiya, tun lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011, a baya-bayan ta fuskanci rigingimun siyasa da matsalar tabarbarewar harkokin tsaro, musamman a gabashin kasar, ciki har da batun halaka jama'a, da na bama-bamai da kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da fararen hula. (Ibrahim)