An yi kira akan kasashen Turai da su kakabawa kasar Rasha takunkumi, a sakamakon matakan da take dauka a Ukraine.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama shi ne ya yi wannan kiran, a yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa, a karshen ganawar da ya yi da firaministan kasar Malaysia Najib Razak, a Kuala Lumpur.
Obama ya jaddada cewar, za su dauki tsauraran mataki na hadin kai tsakanin Turai da Amurka, hakan zai sa shugaba Putin na Rasha ya gane cewar, Amurka da Turai sun hada kai, kuma wannan ba wai fada ba ne na Amurka da Rasha kawai.
Obama ya ce, duk da cewar kasashen duniya sun rattaba hannu akan yarjejeniyar hana yaduwar rikicin na Ukraine, kasar Rasha ta kasa yin wani hobbasa wajen kashe wutar rikicin, shugaban na Amurka ya ce, akwai kuma kwararan sheda dake nuni da cewar, Rasha na da hannu wajen ba da damar abkuwar abubuwan dake wakana a Ukraine.
Shi dai shugaban kasar ta Amurka, tun a ranar Asabar ne ya fara yin wata ziyarar aiki ta kwanaki ukku, a Malaysia. (Suwaiba)