in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama wani babban kwamandan Boko Haram a Nigeriya
2014-07-16 09:19:49 cri

Rundunar 'yan sanda a Nigeriya sun sanar da kama Mohammed Zakari, wani babban kwamandan kungiyar 'yan Boko Haram, dake da alhakin kai hare-haren da mutane da dama suka mutu tun daga shekarar 2009.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya fitar, kuma kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu, Mohammed Zakari, 'dan shekaru 30, ana zargin hannun shi a cikin kisan wasu mutane 7 da suka hada da mata da yara.

Wanda ake zargin an dai kama shi ne ranar Asabar din da ta gabata lokacin da yake kokarin tserewa sakamakon wani farmaki da rundunar tsaron kasar suka kai a maboyar 'yan kungiyar dake dajin Balmo a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar, in ji Mr. Mba.

A cewar kakakin, shi dai wannan kwamandan ya samu horo ne daga wajen wani mai suna Abba Taura a jihar Gombe, kuma ya yi kaura zuwa dajin Balmon ne watanni uku da suka gabata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China