in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana goyon baya ga kare ikon yankunan Iraqi
2014-07-08 09:46:23 cri

Manzon kasar Sin a Gabas ta Tsakiya Wu Sike ya bayyana aniyar kasarsa ta goyawa mahukuntan kasar Iraqi baya, a yunkurinsu na kare ikon cin gashin kai, da yaki da ayyukan ta'addanci.

Mr. Wu ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da firaministan kasar Iraqi Nouri al-Maliki, inda suka yi musayar ra'ayoyi game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da Iraqi ke ciki a halin yanzu, game da kokarin dakile ayyukan mayakan Sunni dake burin raba kasar.

Manzon kasar ta Sin ya kuma bayyana cewa, kasarsa ta bukaci daukacin kasashen duniya, da su kara yawan taimakon da suke baiwa Iraqi, kamar dai yadda hakan ke daidai da kudurin kare 'yancin kan daukacin kasashen duniya baki daya.

Da yake tsokaci game da irin gudummawar da Sin ke baiwa kasarsa, firaministan Maliki ya bayyana godiya da yabon mahukuntan Iraqin, yana mai cewa, hakan ya nuna irin damuwa da Sin ke yi game da halin da Iraqi ta shiga, musamman ma a wannan mawuyacin lokaci.

Kaza lika Maliki ya bukaci kasar Sin da ta shiga aikin sake ginin kasar, kasancewar a cewarsa, gwamnatin sa, za ta yi iyakacin kokarin ganin an ba da kariya ga kamfanonin Sinawa da ma'aikatansu, a dukkanin fadin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China