Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, tana shirin maido da kasar Madagascar cikin kungiyar, bayan dakatar da ita shekaru 4 da suka gabata, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Wannan bayani ne na kunshe ne cikin wata wasika da hukumar zartaswar kungiyar ta aikawa sabon shugaban kasar da aka zaba Hey Rajaonarimampianina, inda ta ce tana shirin gayyatar kasar ta Madagascar da ta dawo a ci gaba da dama wa da ita cikin ayyukan kungiyar, bayan sabon shugaban ya fara aiki.
Kwamitin kungiyar mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro, ya yabawa al'ummar kasar Madagascar, masu ruwa da tsaki a bangaren siyasar kasar, bisa ga sadaukarwar da suka nuna, wadda ta kawo karshen gwamnatin wucin gadin kasar ta hanyar gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu cikin nasara.
Shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU, ta yi kira ga kasashen duniya, da su taimakawa kasar Madagascra, a kokarin da take yi na farfado da harkokin rayuwar jama'a, tattalin arziki da kuma sasanta 'yan kasa. (Ibrahim)