Hedkwatar tattalin arzikin kasar Benin, wato Cotonou za ta karbi bakuncin babban taron ministoci kan sabuwar manufar dangantaka domin karfafa karfin sarrafawar kasashen da ba su da saurin cigaba, daga ranakun 28 zuwa 31 ga watan Yuli, in ji wata majiyar diplomasiyya.
A cewar wannan majiya ta kusa da ma'aikatar karkokin wajen kasar Benin, wannan dandali zai tattara wakilai fiye da 300 daga kasashe 49 da ba su da saurin cigaba, har ma da kungiyoyin ba da tallafin cigaba, bangaren masana'antu masu zaman kansu da manyan jami'ai.
Makasudin wannan zaman taro, shi ne na kafa wasu muhimman hanyoyi da karfafa musanya ta hanyar danganta tsakanin kudu da kudu, tare kuma da karfafa dangantakar arewa da kudu da samar da fasahohi.
Haka kuma wannan dandali zai kasance wata babbar dama wajen tattauna dabarun da za su taimakawa tallafin kudade da sauran hanyoyin taimako da ake samu wajen yin amfani da su, ta yadda za su ba da wata babbar gudunmuwa ga aza tubulin samun cigaban tattalin arziki mai karfi kuma cikin sauri. (Maman Ada)