Shugaban kasar Benin, Boni Yayi dake jagorantar kamfen fadakarwa tun daga wuraren da ake noman auduga dake yankunan arewacin kasar, ya bukaci manoman kasar da su kara himma da kwazo domin kai ga samar da tan dubu dari hudu na auduga na kamfen shekarar 2014 zuwa ta 2015, in ji rediyon gwamnatin kasar a ranar Laraba.
Yan uwanmu manoma, in yi kira da ku rubanya kokari domin shuke a kalla fadin hekta dubu 400 na auduga a kamfen noman shekarar bana domin cimma nasarar kai ga samun tan dubu dari hudu na auduga, ta yadda za a bunkasa cigaban tattalin arzikin kasarmu da ya kai adadin kashi 5,7 cikin 100, in ji shugaba Boni Yayi. (Maman Ada)