in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin na fatan ganin an soke hukuncin kisa a wasu kasashen Afrika
2014-07-03 10:43:18 cri

Ministan harkokin wajen kasar Benin, Nassirou Arifari Bako, ya yi kira a ranar Laraba ga kasashen Afrika, inda ake cigaba da aiwatar da hukuncin kisa da rubanya kokari domin cimma matakan soke wannan hukunci, tare da maye gurbinsa da hukunce-hukuncen da suka dace dake la'akari da girmama 'dan adam da cigaba.

Mun san cewa, ko wace al'umma na da halayya da ra'ayi na musammun game da batun hukuncin kisa, duk da kokarin da duniya ke yi wajen kawar da wannan hukuncin, amma har yanzu akwai inda ake cigaba da aiki da wannan hukunci a wasu kasashen Afrika, in ji ministan tare da yin kira ga wadannan kasashen Afrika da su soke hukuncin, ko maye gurbinsa da wasu hukunce-hukuncen masu sassauci.

Da yake magana a yayin bikin bude taron shiyya kan soke dokar hukuncin kisa a Afrika, shugaban diplomassiyar kasar Benin ya nuna cewa, wannan aiki ne mai wuya, amma ba wanda za'a kasa ba idan aka yi la'akari da rungumar tsarin demokaradiyya da yawancin kasashen Afrika suka yi, da kuma niyyarsu na gina wasu kasashe masu 'yanci, inda a cikinsu, girmama 'yancin rayuwa ke da babban muhimmanci, tare da kare 'yancin jama'a, girmama dajarar 'dan adam da sauransu.

A cewar kwamitin kare hakkin 'dan adam da al'umma na Afrika, kasashen Afrika 16 ne suka soke hukuncin kisa, 23 na shawarar daukar wannan mataki, kana kasashe 17 sun kada kuri'ar da ta shafi kudurorin MDD dake kiran kasashen duniya da su aiwatar da kundin dakatar da hukuncin kisa da aka cimma a ranar 21 ga watan Disamban shekarar 2010. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China