in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Sin ya gana da kusa a jam'iyya mai mulki a Tanzania
2014-06-25 10:36:56 cri

Yayin ziyarar aiki da ya gudanar a kasar Tanzania, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, ya bayyana bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin JKS da jam'iyyar CCM mai mulki a Tanzania.

Mr. Li wanda ya yi wannan tsokaci yayin da yake zantawa da mataimakin shugaban jam'iyyar ta CCM Philip Mangula, ya gabatar da wasu shawarwari guda 3, wadanda a cewarsa za su taimaka wajen habaka dangantakar dake tsakanin jam'iyyun biyu.

Wadannan shawarwari dai sun hada da tattaunawa da amincewa da juna tsakanin jam'iyyun, da musayar fasahohin gudanarwa, da kuma aiwatar da muhimman kudurori tare, ta yadda hakan zai ba da damar fadada dangantakar Sin da nahiyar Afirka baki daya.

Da yake mai da martani game da kalaman mataimakin shugaban kasar ta Sin, Philip Mangula ya ce, jam'iyyun kasashen biyu na samun karin fahimtar juna, da bunkasar hadin gwiwa, tun bayan kafuwar huldar kawance tsakaninsu.

Kaza lika Mr. Mangula ya bayyana burin jam'iyyar CCM, game da batun daga matsayin dangantakar dake tsakaninta da JKS zuwa wani sabon mataki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China