Senda Ould Boumama, kakakin kungiyar kishin Islama ta Ansar Dine ya shiga hannun jami'an tsaron kasar Mauritania, a gabashin kasar tare kuma da turo keyarsa zuwa birnin Nouakchott tun rana Litinin bisa kulawar jami'an leken asirin kasar Mauritania, a wani labarin da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ya samu daga wata majiyar jami'an tsaro. Boumama ya kai kansa ga sojojin kasar Mauritania dake Bassiknou kusa da iyaka da kasar Mali a ranar Lahadi, kafin a turo sa Nouakchott.
Kakakin Ansar Dine ya bayyana a ranar 17 ga watan Afrilun da ya gabata cewa, yana da niyyar mika kansa ga jami'an tsaron kasar Aljeriya, a cikin wata hira ta wayar tarho tare da kamfanin dillancin labarai na kasar Mauritania ANI.
Boumama ya bayyana rokonsa ga shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz da gwamnatinsa da su yi kokarin ganin an tusa keyarsa zuwa kasar ta Mauritania domin ya bayyana gaban kotu.
Senda Ould Boumama ya yi suna a farkon mamayewar da 'yan kishin Islama suka yi wa arewacin kasar Mali a matsayinsa na kakakin kungiyar kishin Islama ta Ansar Dine, kafin ya tsere tare da sauran wasu shugabannin kungiyar bayan da kasar Faransa ta tura sojojinta zuwa arewacin kasar Mali domin yakar kungiyar kishin Islama. (Maman Ada)