in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a gudanar da zaben shugaban Mauritaniya a 21 ga Yunin bana
2014-04-22 11:05:05 cri

An tsai da ranar zaben shugaban kasar Mauritaniya zuwa 21 ga wata Junin shekarar 2014 na zagayen farko idan kuma ta kai ga zagaye na biyu, an rike ranar 5 ga watan Juli, a cewar wani kudurin fadar shugaban kasa na ranar Lahadi.

Kudurin ya jaddada cewa, daukar sunayen 'yan takarar zaben shugaban kasa za'a aike su zuwa kotun kolin kasar daga bakin ranar kudurin ya fito kuma ya kamata sunayen su isa kafin ranar Laraba 7 ga watan Mayun shekarar 2014 da dare.

An tsai da ranar zaben shugaban kasa a lokacin da tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa take cikin mawuyacin hali. Haka kuma shugabannin 'yan adawa suka bayyana mamakinsu kan wannan kuduri da a cewarsu, ba zai taimaka ba wajen warware rikicin siyasar da kasar take fama da shi, in ji manazarta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China