Ministan ruwa da tsabtace muhalli na kasar Mauritania, Mohamed Salem Ould Bechir yana ziyarar aiki ta tsawon mako daya tun ranar jiya a nan kasar Sin domin raya hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, a cewar wata majiya a birnin Nouakchott.
A cikin watan Febrairun shekarar 2010 ne aka sanya hannu kan wata yarjejeniyar gudanar da aikin kashin farko na tsabtace birnin Nouakchott a hedkwatar kasar tsakanin ministan da madam Ma Yingying, mataimakiyar darektan kamfanin hadin gwiwar kasa da kasa na Gezhouba na kasar Sin.
Matakin farko na wannan aiki da kamfanin kasar Sin ke gudanarwa ya shafi unguwannin da suke fama da tarewar ruwan datti a lokacin damana, amma kuma har yanzu matsalar tsabta na kasancewa babban kalubale a birnin Nouackchott.
A shekarar 2013, ruwa suka mamaye unguwanni da dama dake birnin Nouakchott, lamarin da ya tilastawa mutane da yawa barin muhallinsu, bayan an samu ruwan sama na tsawon milimita 30.
Matsalar tsabta da kawar da ruwa a lokacin damana ya kasance muhimmin aikin hukumomin Nouakchott da kuma matsalar dake jan birki ga cigaban hedkwatar kasar. (Maman Ada)