in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya gana da wakilin Sin mai kula da harkokin Afrika
2014-04-01 15:11:18 cri

A ranar Litinin ne shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya gana da wakili na musamman na gwamnatin kasar Sin, mai kula da harkokin Afrika Zhong Jianhua a Khartoum.

A yayin ziyarar Zhong, ya mikawa shugaban kasar ta Sudan sakon gaisuwa daga shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Zhong, ya kuma gabatar da godiya ga shugaban kasar na Sudan, a bisa taimakon da gwamnatin kasar ta baiwa ma'aikatan samar da man fetur a Sudan ta Kudu, inda fada ya barke a kwanan nan.

A lokacin taron, bangarorin biyu sun kuma duba gamayyarsu ta diplomasiyya tare da yin musayar ra'ayi a game da halin da ake ciki a Sudan ta Kudu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China