in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Sudan Al-Fatih Alden
2014-04-03 19:40:37 cri
Yau Alhamis 3 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Sudan Al-Fatih Lzz Alden a nan birnin Beijing,fadar gwamnatin kasar inda a lokacin ganawar tasu Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin na kyautata dangantaka tsakaninta da Sudan bisa manyan tsare-tsare da yin hangen nesa.

Shugaba Xi y a ce a don haka kasar take fatan yin kokari tare da Sudan bisa zarafin cika shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, domin zurfafa hadin gwiwa a duk fannoni, da bude sabon babi tsakanin su.

A nasa bangare, Al-Fatih Lzz Alden ya furta cewa, makasudin kawo ziyara a Sin a wannan karo shi ne kara sada zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. Ya ce Sudan na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin a fannonin makamashi, ma'adinai, manyan kayayyaki masu amfanin jama'a da dai sauransu, da kuma kara hadin gwiwa kan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya baki daya.

Ban da haka, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang, shima a yayin da yake ganawa da Al-Fatih Lzz Alden, , ya bayyana cewa, yanzu haka Sin na kokarin tabbatar da tsarin zurfafa yin kwaskwarima a duk fannoni da aka tsara a cikakken zaman taro na uku na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 18, wanda ba ma kawai zai sa kaimi ga samun dauwamammen ci gaba na Sin ba, har ma zai kawo sabon zarafin hadin gwiwa da na bunkasuwa ga Sudan da ma sauran kasashen duniya baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China