A jiya Laraba ne kasashen Habasha da Sin suka bayyana amannar da suka yi na kara bunkasa gamayyar tattalin arziki tsakaninsu.
A ranar Laraba ne dai aka fara gudanar da taro na takwas na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Habasha da Sin a kan gamayyar tattalin arziki, fasaha da kimiyya, da kuma cinikayya, a can birnin Addis Ababa, dake Habasha.
Bayan taron, karamin ministan kudi da raya tattalin arziki na Habasha Ahmed Shide, da mataimakin ministan cinikayyar Sin, Zhang Xiangchen sun shaidawa manema labarai cewar, bangarorin biyu sun gudanar da tattaunawa mai ma'ana a kan bangarori dabam-dabam na hadin gwiwa.
Dukanin jami'an guda biyu sun bayyana cewar, kasashen nasu guda biyu a shirye suke su kara dankon hadin gwiwa tsakaninsu. (Suwaiba)