Wasu mutane da ake zargin da shiga kasar Kenya ba bisa doka ba sun bayyana gaban wata kotun Kenya a ranar Talata. An yanke musu zaman gidan yari na shekaru biyu, ko kuma a sake su bayan da suka biya tarar dalar Amurka 114.300. Kuma za'a tusa keyarsu kasarsu idan kusa kammala wa'adin hukuncin nasu. 'Yan kasar waje da dama ne suka amsa kiran jami'an tsaron kasar Kenya a Hadado.
Mutanen sun fito daga birnin Moyale dake kan iyaka da kasashen biyu domin isa birnin Nairobi, a cewar kwamandan 'yan sanda na shiyyar Wajir, mista David Kirui. 'Yan kasar Habasha 32, aka maida kasarsu a makon da ya gabata bayan sun kare zaman yajinsu na watanni shida. 'Yan sandar shiyyar Wajir na fama da matsalar kwararowar bakin haure da dama 'yan asalin kasar Habasha dake shiga wannan kasa ta kan iyakar Wajir. (Maman Ada)