in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 41 ne suka rasa rayukansu a hare-hare a Iraki
2014-03-10 12:23:19 cri

A kasar Iraki, an kashe mutane 41, a inda kuma wasu mutane 129 suka sami rauni, a wasu hare-haren da aka kai, wadanda suka hada har da wani babban harin kunar bakin wake, wanda aka kai jiya Lahadi, kamar dai yadda wata majiya ta 'yan sanda da jami'an lafiya suka bayyyana.

A hari guda, an hallaka akalla mutane 34 , tare da raunata wasu mutanen 120, a yayin da wani 'dan harin kunar bakin wake ya tada bama-bamai dake cike da motarsa, a wata cibiyar bincike ta 'yan sanda, wadda take kofar shiga, wani wuri da na gudanar da binciken tarihin, na tsohon birnin Babylon, wanda ke arewacin birnin Hilla, kilomita 100 a kudancin Bagadaza. Wani jami'in 'yan sanda, wanda ya nemi a sirranta sunan shi, shi ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua abin da ya faru.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai kazamin harin, to amma a yawancin lokuta 'yan kungiyar al-Qaida a Iraki, a kan yi zargin suke da hannu wajen aiwatar da munanan hare-hare a kasar ta Iraki, a inda ake fargabar yiwuwar dawowar rikici tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda tare da kungiyoyi masu dauke da makamai.

A shekarun baya-bayan nan dai kasar Iraki ta shiga cikin munanan hare-hare. Kamar dai yadda ofishin agaji na majalisar dinkin duniya ya bayyana, an kashe 'yan kasar ta Iraki, fararen hula da 'yan sanda kimanin 8868 a shekara ta 2013. Adadi mafi yawa a cikin shekaru da dama da suka gabata. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China