in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Libya ta yi gargadi kan barazanar dake neman janyo rabuwar kasar
2014-07-26 16:15:15 cri
Ganin yadda wasu kungiyoyin dakaru ke dinga arangama da juna a kasar Libya, gwamnatin wucin gadin kasar ta ba da wata sanarwa a Jumma'a 25 ga wata, inda ta yi gargadi kan yadda dauki-ba-dadin ke janyo wa kasar baraka.

Wani kakakin gwamnatin ya sanar da hakan a taron manema labarun da ya gudana a ranar Jumma'a, haka kuma ya nanata cewa, idan aka samu rabuwar kasa, to za a tsunduma al'ummarta cikin wani yanayi na yaki maras karshe, abin da zai janyo barna matuka.

Tun bayan da aka hambarar da mulkin Ghadafi a shekarar 2011, filin saukar jiragen sama dake Tripoli, fadar mulkin kasar, ya fara zama hannun dakarun kungiyar Zintan, wadanda ba su da wata akidar musamman kan addini. Amma daga ranar 13 na watan da muke ciki, wasu kungiyoyin dakaru masu ra'ayin addini, ciki har da kungiyar Misrata, sun fara kai hari ga filin saukar jirgin saman. Zuwa ranar Jumma'a, an riga an kwashe kwanaki 13 ana artabu da juna.

Kungiyoyin 2 da ke arangama da juna, wato Zintan da Misrata, sun kasance kungiyoyin dakaru mafi karfi a kasar Libya. Ganin haka da kuma yadda ake ta samun rikice-rikice a birnin Banghazi dake gabashin kasar, sun sa ana nuna damuwa kan yiwuwar sake abkuwar yakin basasa a kasar ta Libya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China