Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, cutar Ebola na ci gaba da yaduwa a Afrika, saboda wadansu tsoffin al'adu da addinai na gargajiya.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce, wadansu al'adun da ake yi sun sabawa matakan da aka jera na hana yaduwar cutar.
Darektan ofishin hukumar lafiya ta duniya a yankin Afrika, Luis Gomes Sambo, shi ne ya bayyana hakan a jawabinsa na bude wani taron ministoci na gaggawa a kan bazuwar cutar Ebola a yammcin Afrika, wanda hukumar lafiya ta duniya ta shirya a jiya Laraba.
Ana sa ran taron na kwanaki biyu, ya samu halarcin ministocin lafiya na kasashe 11, da kuma kasashen waje, dake aiki tare da kasashen na Afrika a kokarin da ake yi na dakile cutar ta Ebola mai saurin kashe jama'a a kan lokaci. (Suwaiba)