in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO na aiki tukuru domin murkushe barkewar cutar Ebola a Guinea
2014-04-02 14:09:02 cri

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, wacce ke karkashin majalisar dinkin duniya na gudanar da kokarin dakatar da ci gaban yaduwar cutar Ebola, a kasar Guinea.

Wannan mataki na majalisar dinkin duniyar, ya biyo bayan karuwar yawan wadanda ake zargin sun kamu da cutar, da kuma yawaitar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ta Guinea, wacce ke yammmacin Afrika, a inda a halin da ake ciki, adadin wadanda suka kamu da cutar sun haura adadi 103, da aka samu tun farko, ya zuwa mutane 122, a cikin kwanaki uku, kuma tuni aka tabbatar da mutuwar 80 daga cikin wadanda suka kamu da cutar, kamar dai yadda jami'an na majalisar ta dinkin duniya suka tabbatar.

Kakakin hukumar lafiya ta duniya, Gregory Hartl ya ce, lokacin kyankkyashewar kwayoyin cutar Ebola ya kai kwanaki 2 ne zuwa 21, kuma tuni hukumar lafiyar ta duniya ta kara yawan adadin kwanaki da cutar take yi kafin ta yadu, domin ta sami tsawon lokacin da ake bukata na tabbatar da cewa, ba'a samu yaduwar cutar ba.

Gregory Hartl ya ce, akwai mahimmancin gaske wajen ganin an wayar dukkan jama'ar kasar, tare da ilmantar da su. Ya ce, duk da yake cewar a wanann karon, yaduwar cutar ba ta kai yawan da aka taba samu a can baya ba, na kasashen jamhuriyar demokradiyyar Congo, da kasar Uganda, to amma salon barkewar cutar ya yi daidai da yadda aka rinka samun yaduwar cutar a can baya. Shi dai kakakin na hukumar lafiyar ta duniya ya nanata cewar, abu mafi mahimmanci shi ne a dakatar da yaduwar cutar, tare da gano dukanin wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar.

Gregory Hartl ya ce, barkewar cutar a wannan karon a kasar Guinea, ba ta kai matakin da ke yin barazana ba na yaduwa, kamar yadda ya ce, wannan shi ya sa hukumar ba ta bayar da shawara ta gindaya shingen bulaguro, ko kasuwanci ba a kasar ta Guinea. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China