Ministan kiwon lafiyar kasar Saliyo ya tabbatar a ranar Litinin cewa, mutum guda ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a yankin gabashin kasar, kusa da kan iyaka da kasar Guinea.
Mista Brima Kargbo, jami'in kiwon lafiya, ya bayyana cewa, a tsawon makon da ya gabata, mutane kusan 11 a kauyen Kailahun, kusa da iyaka da kasar Guinea, sun yi fama da amai da gudawa masu tsanani. Tuni dai aka isa da jininsu zuwa cibiyar bincike ta Kenema dake gabashin kasar, mai tazarar kilomita 300 daga Freetown, babban birnin kasar in ji mista Kargbo a cikin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Kuma bincikin na cibiyar Kerema ya tabbatar da cewa, mutum guda na dauke da cutar ta Ebola, kana sauran mutane uku kuwa, ba'a tabbatar da cewa, har yanzu ko suna dauke da cutar ko a'a, in ji mista Kargbo. (Maman Ada)