in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kan iyakar Ghana ba zai bude ba ga 'yan ta'adda, in ji shugaban kasar
2014-05-09 11:12:46 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ce, yana nan a kan bakansa, na sadaukarwar da ya yi, a kan karfafa rawar da kasar Ghana ke takawa ta samar da zaman lafiya a Afrika ta yamma, da kuma duniya baki daya.

Shugaban kasar ta Ghana Mahama, wanda yake jawabi ga al'umar kasarsa, a game da sha'anin tsaro ya ce, kan iyakar kasar Ghana a kulle yake ga 'yan ta'adda, a inda ya kara da cewar, kasar Ghana ba za ta boye wadanda suka yi wani laifi ba, kuma ba za ta lamunta ba su mayar da kasar ta rumbu na aje makamai.

Fiye da 'yan mata dari 2 ne dai aka sace a watan Aprilu, a garin Chibok, dake jihar Borno, wacce ke arewa maso gabashin Nigeria.

A Litinin din da ta gabata, kungiyar Boko Haram ta Nigeriya, ta yi ikirarin cewar, ita ce ke da alhakin sace 'yan matan, kuma ta yi barazana za ta sayar da su a kasuwa.

Shugaban kasar ta Ghana ya ce, a saboda abun da ke faruwa a yankin Afrika ta yamma, ya umurci majalisar tsaro ta kasar da ta karfafa tare da inganta matakai na tsaro, da kuma tabbatar da cewa, suna gudanar da sintiri a duk fadin kasar ta Ghana, domin a tabbatar da cewar, duk wanda zai shiga Ghana zai shiga kasar ne da dalili dake kan tsarin doka. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China