Daruruwan mata ne suka gudanar da wata zanga-zanga ta lumana, domin nuna rashin jin dadinsu a game da matakin da kungiyar Boko Haram ta dauka na sace wasu daliban sakandare 'yan mata 200 a Najeriya.
Matan sun yi jerin gwano, ta hanyar zagayawa wasu manyan tituna dake Accra, babban birnin kasar Ghana, a inda suka kammala zanga-zangar a babban ofishin huldar jakadanci na Najeriya dake Ghana, kuma suka gabatar wa ofishin, da wata takarda mai sa hannun mutane 300, wacce ta nuna kin amincewa da matakin sace 'yan matan na Najeriya.
Takardar koken ta yi kira a kan gwamnatin Najeriya da ta tashi haikan domin ganin an ceto 'yan matan da aka sace.
Hakazalika, takardar koken ta kuma bukaci babban kwamishinan dake shugabantar ofishin huldar jakadancin na Najeriya da ya yi matsin lamba a kan gwamnatin kasar domin ta dauki duk matakin da ya dace, wanda ke karkashin ikon ta, ta taimaka ta maido da 'yan matan da aka sace.
A nashi bangaren, babbban kwamishinan dake shugabantar ofishin huldar jakadanci na Najeriya a Ghana Ademola Oluseyi Onafonoka, bayan da ya karbi takardar koken, ya kuma tabbatar wa masu zanga-zangar cewar, gwamnatin Najeriya na gudanar da aiki tukuru domin ganin an maido 'yan matan da aka sace. (Suwaiba)