in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sallar idi a masallacin Niujie da ke birnin Beijing
2014-07-29 16:51:20 cri

Ranar yau muhimmiyar rana ce ga kowa ne musulmi, kuma lokaci mai muhimmanci ga rayuwar musulmi, dalilin da ya sanya masallancin Nuijie ya cika makil da jama'ar musulmin kasar Sin da kuma musulmi 'yan kasashen waje wadanda suka daga kasashen larabara, Asiya, Afrika da ma na wasu sassan duniya dake aiki anan kasar Sin inda suka yi harama wuri daya cikin jituwa kuma karkashin laima guda ta addinin musulmuci domin karrama wannan rana. Kamran Bodla dan Pakistan ne da ke dalibta a nan birnin Beijing, kuma ya ce, wannan ne karo na farko da yake yin karamar sallah a nan birnin Beijing, amma irin yanayin da ake gudanar da bikin gaskiya ya burge shi, ya ce, "Yau ne ake bikin sallar idi, kuma mun zo nan ne mu yi sallah. Na yi farin ciki sosai da haduwa da 'yan uwa musulmi masu dimbin yawa a nan. Wannan ne karo na farko da na yi bikin karamar sallah a nan kasar Sin, da farko, na dan yi kewan gida, amma da na zo nan, gaskiya na ji dadin irin yanayin bikin sosai. Jama'ar kasar Sin suna da zumunci, kuma musulmin da ke nan dukkansu kamar iyalaina ne."

1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China