in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sallar idi a masallacin Niujie da ke birnin Beijing
2014-07-29 16:51:20 cri

A nan birnin Beijing, daruruwan musulmi da yawansu ya kai kimanin dubu shida ne a yau suka kwarara zuwa babban masallacin Nuijie dake nan birnin Beijing cikin farin ciki da annashuwa, masallacin da ya kasance mafi dadadden tarihi da kuma girma a nan birnin Beijing, domin gudanar da sallar Idi da ta kasance cikamakin kawo karshen kusan wata guda na Azumi musammun ma ga musulmin dake nan kasar Sin, inda tsawon wata guda musulmi suka kauracewa ci da sha bisa ibada domin neman gafarar Allah da kuma neman alfarmar dake cikin watan Ramadan. Maza da mata, yaro da babba kowa sanye da tufafi masu kyaun gani, tun da sayin safiya suke isa babban masallacin Nuijie da zummar gudanar da sallar Idi dake bayyana karshen watan Ramadan. A cikin masallacin, mun hadu da wani saurayi dan kabilar Hui, wanda dalibi ne da ke karatun harshen Larabci a jami'ar koyar da harsunan waje ta Tianjin, kuma ya dawo gidansa a birnin na Beijing cikin wannan lokacin hutu na yanayin zafi, ga shi kuma ya zo masallacin ne domin bikin sallar idi. A lokacin da muka tabo magana a kan watan azumin da ya kare kwanan nan, ya ce,"A farkon lokacin shiga watan azumi, ba mu fara hutu ba tukuna, kuma an fara samar da horaswar aikin soja a jami'armu. To, amma ga shi mu musulmi mun fara azumi, shi ya sa shugabannin jami'armu sun ba mu taimako, sun ce ba sai mu shiga horaswa ba, sai mu yi kallo ne kawai. Don haka, na yi kwanaki sama da 10 a jami'a, daga baya, na koma gida, na yi azumi tare da sauran iyalaina."

1 2 3 4 5 6 7 8 9
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China