Kungiyar ma'aikata mafi rinjaye a kasar Afrika ta Kudu a ranar Lahadin nan ta sanar da cewa, za ta fara gagarumin yajin aikin da ta shirya a bangaren karafa da injiniya a mako nan da aka shiga.
Babbar kungiyar ma'aikatan a sassan karafa NUMSA ta sanar da hakan bayan da tattaunawa game da karin albashi ya ci tura. Kamar yadda babban sakataren kungiyar Irvin Jim ya sanar ya ce, shugabannin kungiyar sun amince da a tafi yajin aikin na sai baba ya gani tun daga ranar Talata.
Mr. Jim a lokacin da yake ganawa da manema labarai ya ce, wannan shawara ba mai sauki ba ne, kuma akwai matukar wuya, amma ba su da zabi ganin cewa, a wannan lokacin, shugabannin ma'aikatar nasu za su aiwatar da dokar ba aiki ba albashi.
Kungiyar ma'aikatar dai ta bukaci karin albashi da kashi 12 a cikin 100 kusan ninki biyu a kan albashin yanzu, amma mahukuntar ma'aikatunsu suka amince da kashi 5.6.
Yanzu haka dai kusan ma'aikata 220,000 daga cikin 300,000 na sashen karafa ake sa ran za su shiga cikin yajin aikin na gama gari. (Fatimah)




