Manyan kamfanonin Afrika ta Kudu da ma'aikatan dake yajin aiki za su sake kawo teburin shawarwari a ranar Talata mai zuwa domin kawo karshen cigaban yaki aiki, in ji wata mijiya ta kusa da wadannan kamfanoni a ranar Litinin.
Batutuwan za su mai da hankali kan wata mafita da kamfanin Anglo American Platium (Amplats), Impala Platium (Implats) da Lonmin suka gabatar, in ji kakakin kamfanin Implats, Johan Theron.
Kamfanonin uku sun gabatar da mafitar da ta shafi batun gyara kan albashi da alfarma kan wasu fannonin zaman rayuwar ma'aikata mambobin kungiyar AMCU, wato kungiyar kwadagon hakar ma'adanan kasar.
A cewar wannan sabuwar mafita, karin kudin albashi da aka yi niyya zai taimaka ga samun gwargwadon albashi ga ma'aikatan dake aiki karkashin kasa na Rands 12500 a kowane wata, kwatankwacin dalar Amurka 1190, ko Rands dubu 150 a kowace shekara wato kimanin dalar Amurka 14280 a shakarar 2017. (Maman Ada)