in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar 'yan kwadagon Afirka ta Kudu ta yi barazanar tsananta yajin aiki
2014-07-17 09:55:57 cri

Babbar kungiyar 'yan kwadago ta kasar Afirka ta Kudu ta yi barazanar tsananta yajin aikin da take yi, sakamakon janye karin albashi da kungiyar masu masana'antun sarrafa karafa da na gine-gine suka yi.

Kungiyar 'yan kwadagon ta NUMSA a takaice, ta zargi kungiyar SEIFSA mai iko da sashen da warware alkawarin da ta yi tun da fari, na samarwa ma'aikatan sashen karin albashi.

A cewar mai magana da yawun kungiyar ta NUMSA Castro Ngobese, kungiyar SEIFSA ce za ta dauki alhakin dukkanin abin da ya biyo bayan yajin aikin nasu. Sai dai a daya bangaren, babban jami'ar kungiyar ta SEIFSA Kaizer Nyatsumba, cewa ya yi, karin albashin da aka ambata a makon da ya gabata ya gaza kawo karshen yajin aikin da ma'aikatan ke yi, hakan ne kuma ya sa aka janye shi.

SEIFSA dai ta gabatarwa ma'aikatan karin kashi 10 bisa dari ne a bana, sai kuma karin kashi 9.5 bisa dari a shekarar 2015, da kuma na kashi 9 bisa dari a shekarar 2016, matakin da NUMSA ta ce sam ba ta amince da shi ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China