in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da yadda Libya ta bayyana sakamakon zaben majalisar wakilan jama'ar kasar
2014-07-24 14:35:19 cri
A yau Alhamis 24 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi maraba da sakamakon zaben majalisar wakilan jama'ar kasar da Libya ta sanar. Haka zakila, Sin tana son ci gaba da taimaka wa kasar wajen ciyar da yunkurin mika mulki da farfado da tattalin arzikin kasar.

Ya kuma kara da cewa, kasar Libya sahihiyar kawar kasar Sin ce, Sin na fatan bangarori daban daban da rikicin kasar ya shafa za su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari a siyasance, bisa ka'idar kiyaye babbar moriyar kasar da jama'arta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China