in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da yin musayar wuta don kwace filin jiragen saman kasar Libya
2014-07-24 10:49:45 cri
Dakaru masu goyon bayan bangaren al'ummar kasar Libya da dakaru masu kishin addini na kasar sun ci gaba da yin musayar wuta a ranar 23 ga wata a kokarin kwace filin jiragen saman kasar dake Tripoli, babban birnin kasar.

Dakarun sun yi musayar wuta a wani wurin da ke kusa da filin jiragen saman, da bisa hanyar da ke tsakanin birnin da filin jiragen saman, lamarin da ya haddasa wani dakin ajiye man fetur dake dab da hanyar motocin ya kama wuta.

Sakamakon rufe filin jiragen saman kasar da aka yi, ya sa gwamnatin wucin gadin kasar ta bude filin jiragen saman soja na MITI Jia dake birnin Tripoli. Ganin cewa filin jiragen saman karami ne, shi ya sa ba ya iya daukar jiragen sama da dama, dalilin da ya sa sanya fasinjoji suke zama jira a filin jiragen saman. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China