in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kiran Falesdinawa da Yahudawa da su kai zuciya nesa
2014-07-09 12:53:09 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Talata da tsanancewar rikici tsakanin Falesdinawa da Yahudawa, tare da hare-haren rokoki kan Isra'ila tun daga Gaza da kuma luguden wuta ta jiragen sama kan Gaza.

Shugaban MDD ya jaddada kiransa ga dukkan bangarorin da wannan rikici ya shafa da su kai zuciya nesa domin kaucewa wasu sabbin asarar rayukan fararen hula, da kuma kaucewa bazuwar tashen-tashen hankali a wannan yanki baki daya.

Mista Ban ya sake jaddada cewa, ya zama wajibi a maido da zaman lafiya. Dole tashe-tashen hankalin dake faruwa a yankin Gaza, su zama abin da za'a mai da hankali ta bangarorin siyasa, tsaro, jin kai da cigaba wajen neman hanyoyin cimma mafita mai karko a wannan shiyya, in ji kakakin Ban Ki-moon. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China