in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi allah wadai da rikici da ya faru a filin jiragen sama na duniya a kasar Libya
2014-07-18 15:06:20 cri

A ranar 17 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya bayar da wata sanarwa ga manema labaru, inda ya zargi rikicin nuna karfin tuwo a filin jiragen sama na duniya a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya, kuma ya yi kira ga bangarori daban daban na Libya da su yi shawarwari ta hanyar siyasa.

Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya lura da cewa, rikicin da ya barke a filin jiragen sama a babban brinin kasar Libya, zai cigaba da janyo tashe-tashen hankula cikin dogon lokaci a tsakanin mayakan sa kai da hukumomin kasar, kuma lamarin zai kara zama aiki mai wuya wajen tafiyar da harkokin tsakanin bangarorin dake gaba da juna a kasar. Kwamitin sulhu ya yi maraba da zaben majalisar wakilan jama'a da kasar ta gudanar cikin nasara a ranar 25 ga watan Yuni, kuma ya yi kira ga majalisar da ta samu ra'ayi daya tun da wurin wajen kafa wata sabuwar gwamnatin hadin kan 'yan kasa.

A wannan rana kuma, kwamitin sulhu ya shirya wani taro kan halin da ake ciki a Libya, inda aka saurari rahoto daga manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Libya Mista Tarek Mitri ta hanyar bidiyo, inda Mitri ya ce, a halin yanzu manyan rukunoni biyu na mayakan sa kai suna ci gaba da rikici da juna a filin jiragen sama, sun yi watsi da kiraye kirayen gwamnatin wucin gadi ta Libya wajen tsagaita bude wuta. Tuni tawagar MDD dake kasar Libya ta janye ma'aikatanta daga wannan kasa cikin dan gajeren lokaci, amma duk da haka suna cigaba da tuntubar jam'iyyu da kungiyoyi daban daban na kasar Libya, domin sassauta halin da ake ciki a wanna kasa. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China