A kalla jama'a 30 ne suka rasa rayukansu a jiya Lahadin a yayin da wadansu 'yan bindiga suka kai hari a kan wuraren ibada na coci, dake wasu kauyuka biyu a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeria.
Majiyoyin tsaro da wadanda aka yi abin kan idanunsu, sun ce, wadanda aka kashe sun hada da mazauna kauyukan da kuma wadanda suka je coci, a kauyukan wadanda ke kusa da garin Chibok, inda a nan ne, a kwanan baya, aka sace wasu 'yan mata 200 na sakandaren garin. (Suwaiba)