in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a kawo karshen tashin hankali a CAR
2014-05-30 09:44:52 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Alhamis, kan hare-haren baya bayan nan a kasar Afrika ta Tsakiya CAR tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jinni ba tare da bata lokaci ba a cikin wannan kasa.

Mista Ban, ya yi allawadai da harin da aka kai kan cocin "Notre-Dame" na Fatima dake birnin Bangui, inda aka kashe mutane da dama, har da wani fasto daga cikinsu, haka kuma maharan sun yi awon gaba da wasu mutane.

Wannan hari ya zo daidai a yayin sake barkewar sabbin tashe-tashen hankali a babban birnin kasar ta Afrika ta Tsakiya tun farko mako, inda 'yan anti-Balaka suka kashe wasu musulmai uku a yayin da suke kan hanyar zuwa wasan kwallon kafa dake manufar sasanta bangarorin biyu.

Shugaban MDD na goyon bayan hukumomin wucin gadi na kasar kan kokarin da suke yi na kawo karshen tashen-tashen hankali a birnin Bangui, da ma sauran yankunan kasar baki daya, tare da daukar matakan da suka wajaba na gurfanar da dukkan shugabannin bangarorin biyu dake da hannu cikin tashe-tashen hankalin na addini dake barazanar raba kasar biyu, in ji kakakin Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China