in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maiteeq ya sanar da sake shiga takara a zaben firaministan gwamnatin wucin gadi ta kasar Libya
2014-07-08 10:10:59 cri
Dan siyasar nan mai suna Ahmed Maiteeq da kotun koli ta kasar Libya ta yanke masa hukunci bisa saba wa kundin tsarin mulkin kasar a yayin zaben firaministan gwamnatin wucin gadin kasar ya sanar a ranar 7 ga wata cewa, zai sake shiga takara a zaben firaministan gwamnatin wucin gadin kasar da za a yi.

Maiteeq ya bayyana a birnin Tripoli a wannan rana cewa, bayan da ya tattauna da tawagar mashawarta, ya tsaida kudurin sake shiga takara a zaben firaministan gwamnatin wucin gadi ta kasar da za a yi bayan da aka kafa majalisar wakilan jama'ar kasar.

Ban da wannan kuma, Maiteeq ya ce, ana bukatar sabbin shugabanni a kasar Libya, kuma tawagarsa tana da kwarewa da karfin jagorancin kasar har ma da magance matsalolin siyasa da tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Majalisar wakilan jama'ar kasar Libya ce za ta zabi sabon firaministan gwamnatin wucin gadin kasar. An gudanar da zaben majalisar wakilan jama'ar kasar a ranar 25 ga watan Yuni, ana sa ran cewa, za a gabatar da sakamakon zaben a ranar 20 ga wannan wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China