in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya zaben majalisar dokokin kasar Libya a ranar 25 ga watan Yuni
2014-05-30 14:33:42 cri
Shugaban hukumar zaben kasar Libya Imad Sayeh ya sanar a ranar 29 ga wata cewa, majalisar dokokin jama'ar kasar ta wucin gadi ta tabbatar da cewa, za a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga watan Yuni.

Sayeh ya bayyana hakan a gun wani taron manema labaru a wannan rana cewa, za a jefa kuri'a kan zaben a ranar 25 ga watan Yuni, masu zabe 'yan kasar dake kasashen waje kuwa za su jefa nasu kuri'un daga ranar 21 zuwa 22 ga watan Yuni.

Bayan kammala zaben, majalisar dokokin wucin gadi ta kasar za ta mika iko ga sabuwar majalisar dokokin kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China