Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ce, zaben da aka yi a kasar Libya, wata babbar nasara ce, ga kasar wacce ke kokarin komawa kan mulkin damokradiyya.
Shugaban MDD Ban Ki-moon ya ce, zaben 'yan majalisar wakilai da aka yi a Libya, wani babban ci gaba ne a kokarin da ake yi na mai da mulki a hannun wadanda suka dace, tare da samun zaman lafiya a tsarin siyasar kasar.
Kakakin babban sakataren MDD, wanda ya bayyana kalaman na Ban Ki-moon ya ce, Ban Ki-moon ya yi wa jama'ar Libya murna a kan zaben wakilan majalisar dokokin kasar.
A bisa tsarin shirin mai da mulkin siyasa na Libya, sabuwar majalisar dokokin da aka zaba, za ta maye gurbin babbar majalisar hadin kan kasa ta rikon kwarya.
Daga nan kuma sai a gudanar da zaben shugaban kasa, wanda shi ne za'a kammala shirin mai da mulki a hannun gwamnatin da ta dace. (Suwaiba)