in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda za ta bude wasu sabbin ofisoshin jakadanci 5
2014-06-04 10:07:05 cri

Kasar Rwanda ta sanar a ranar Talata cewa, ta nada wani babban shirin bude wasu sabbin ofisoshin jakadanci biyar a cikin wasu kasashen waje, domin kara fadada matsayinta a duniya.

Ministar harkokin wajen kasar Rwanda, madam Louise Mushikiwabo ta yi wannan sanarwa a gaban 'yan majalisun dokokin kasar.

Wadannan sabbin ofisoshin jakadanci biyar, za'a bude su ne a kasashen Angola, Zambiya, jamhuriyyar demokaradiyar Congo, daular Larabawa da kuma Isra'ila, in ji madam Mushikiwabo.

Wannan mataki na da nufin kara bunkasa manufar dangantakar kasa da kasa ta kasar Rwanda zuwa wani matsayin duniya, a cewar babbar jami'ar diplomasiyyar kasar Rwanda tare da nuna cewa, gwamnatin kasarta na yin shawarwari tare da ministocin harkokin wajen wadannan kasashe biyar domin ganin wannan shirin ya fara aiki gadan gadan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China