Babbar jam'iyyar adawa ta Nigeria APC, ta yi suka da kakkausar murya a kan hare-haren baya bayan nan da aka kai Abuja, babban birnin Nigeria da jihar Bauchi, wadanda suka haifar da asarar rayuka 37, tare da raunata wasu mutane da dama.
Kakakin jam'iyyar adawa ta APC, Lai Mohammed ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, jam'iyyar ta bayyana cewar, kungiyar da ke da alhakin kaddamar da hare-haren ta'addancin da ake kaiwa, tana yin wani abu ne kawai na mugunta, da rashin imani da kuma rashin sanin ya kamata.
Mohammed ya ce, babu wata hujja da za ta sanya a dinga zubar da jinin jama'ar kasa, ba tare da wani dalili ba.
Kakakin jam'iyyar ta APC, ya yi kira a kan gwamnatin kasar, da ta kara duba matakan da take dauka, na yaki da ta'addanci, domin kamar yadda ya ce, matakan da gwamnatin ke dauka a halin da ake ciki ba su yin aiki, ko kadan, wannan shi ya sa harin 'yan ta'adda ya zama wani abu, da ake kaiwa a ko wace rana.
Mohammed ya shawarci gwamnati da ta tuntubi dukanin masu ruwa da tsaki na kasar, daga ko wane bangare domin zaburar da matakan yaki da ta'addanci na kasar. (Suwaiba)