Shugaban kasar Nigeriya Goodluck Jonathan ya yi tir da harin bam da aka kai a jihar Bauchi dake arewa maso gabashi da kuma jihar Kaduna da ke tsakiyar arewacin kasar, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi ta bayyana, yana mai jaddada kudurin gwamnatinsa na gurfanar da masu hannu a cikin wannan ta'assa a gaban kuliya.
Shugaban ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda wannan harin ya rutsa da su tare da jajantawa wadanda suka jikkata, ko kuma suka yi asarar dukiyoyinsu a wadannan hare-hare a jihohin biyu.
Sanarwar da ta ce, gwamnati za ta yi iyakacin kokarinta wajen dawo da doka da oda a duk fadin kasar, har ila yau ta yi bayanin cewa, shugaban kasar yanzu haka ya umurci duk sassan da abin ya shafa da su cigaba da ba da agajin gaggawa a bangaren kiwon lafiya da samar da taimakon da ake bukata ga wadanda suka jikkata ko rasa matsugunansu a lokacin wannan harin na bam da makamancin hakan.
Shugaba Goodluck Jonathan daga nan sai ya bukaci daukacin 'yan Nigeriya da su cigaba da ba da goyon bayansu da hadin kai ga sojoji da sauran jami'an tsaro wadanda ke aiki a ko da yaushe wajen ganin an dakile matsalar rashin tsaro a kasar cikin lokacin. (Fatimah)